Connect with us

Sport

Afcon 2021: Egypt ta bayyana wadanda za su buga mata kofin Afirka

Published

on

Masar ta sanar da sunayen ‘yan wasan da za su buga mata gasar cin kofin Afirka da za a fara a Kamaru daga 9 ga watan Janairu.

Cikin ‘yan wasa 25 da ta bayyana ana sa ran Mohamed Salah na Liverpool ne zai yi kyaftin, haka kuma dan kwallon Arsenal, Mohamed Elneny yana daga cikin wadanda za su wakilci kasar a Kamaru.

Sauran ‘yan wasa ukun da ke taka leda a waje sun hada da Ahmed Hegazi mai wasa a Saudi Arabia da Mostafa Mohamed da ke taka leda a Turkiya da kuma Omar Marmoush mai wasa a Jamus.

Advertisement

Mai rike da kofin Afirka karo bakwai za ta fara karawa da Najeriya ranar 11 ga watan Janairu daga baya ta fafata da Guinea-Bissau da kuma Sudan a wasannin cikin rukuni.

Yan wasan Masar da za su buga mata kofin Afirka a Kamaru:

Masu tsaron raga: Mohamed El-Shennawy (Al Ahly, Egypt), Mohamed Sobhi (Pharco, Egypt), Mohamed Abogabal (Zamalek, Egypt), Mahmoud Gad (Enppi, Egypt).

Advertisement

Masu tsaro baya: Ahmed Fatouh, Mahmoud Alaa, Mahmoud Hamdy El-Wensh (all Zamalek, Egypt), Ayman Ashraf, Akram Tawfik, (both Al Ahly), Omar Kamal, Mohamed Abdel-Moneim (both Future, Egypt), Ahmed Hegazi (Ittihad Jeddah, Saudi Arabia).

Masu buga tsakiyaHamdi Fathi, Amr El-Sulya (both Al Ahly, Egypt), Emam Ashour, Ahmed Sayed Zizo (both Zamalek, Egypt), Abdallah El-Said, Ramadan Sobhi (both Pyramids, Egypt), Mohamed Elneny (Arsenal, England), Omar Marmoush (VfB Stuttgart, Germany), Mohanad Lasheen (Tala’a El-Gaish, Egypt), Mahmoud Hassan Trezeguet (Aston Villa, England).

Masu cin kwallaye: Mostafa Mohamed (Galatasaray, Turkey), Mohamed Sherif (Al Ahly, Egypt), Mohamed Salah (Liverpool, England).

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *