Connect with us

News

Karairayin da gwamnatin Buhari ta yi wa ‘yan Najeriya – PDP

Published

on

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta mayar da martani kan nasarorin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi iƙirarin ta samu a 2021, tana mai cewa galibinsu ‘ƙarya ne’

PDP ta kira nasarorin da ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed ya bayyana a ranar Alhamis a “matsayin ƙarya daga gwamnatin da ta gaza.”

“Iƙirarin nasara da gwamnatin APC ta yi babban abin dariya ne na shekara.”

A wani taron manema labarai da ya gudanar, ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce duk da an fuskanci ƙalubale na tsaro da ta tattalin arziki a shekarar 2021, amma gwamnatin Buhari ta samu nasara a fannoni da dama.Ministan ya bayyana nasarorin gwamnatinsu ta APC a fannin tsaro da tattalin arziki da ayyukan ci gaba. Kuma ya takaita nasarorin APC ne kawai a 2021.

Sai dai a wata sanarwa mai taken “Iƙirarin nasarorin gwamnatin tarayya a 2021, ƙarya ne kawai,” PDP ta mayar da martani kamar haka:

  • Tsaro

Game da nasarorin tsaro da APC ta bayyana yawan mayaƙa da aka kashe 1,000 a arewa maso gabas da ƴan bindiga a arewa maso gabashi 427 da kuma yawan mayaƙan Boko Haram 22,000 da suka miƙa wuya, PDP ta ce “gwamnatin da ake kashe jama’arta bai kamata ta fito tana murna da yabon kanta ba duk da gazawarta yayin da ƴan ta’adda suka addabi al’umma.”

  • Tattalin arziki

Ta fuskar tattalin arzki, PDP ta ce ta bar wa APC tattalin arzikin da ya kai dala biliyan 550 mafi girma a Afirka a 2015, amma ƙasar ta koma cibiyar talauci a duniya saboda rashin iya gudanar da mulki da rashawa da riƙon sakainar kashi na gwamnatin APC.

PDP ta ce a 2015 ana bin Najeriya bashin dala biliyan 7.3 amma a yanzu cikin shekara shida bashin ya kai sama da dala biliyan 38.

Jam’iyyar hamayyar ta kuma ce, gwamnatin APC ba ta da abin cewa, saboda a ƙarƙashin mulkin jam’iyyar darajar naira ta faɗi kan dalar Amurka daga N198 a 2015 zuwa N500 a yanzu. Kuma farashin kayan masarufi sun yi tashin gauron zabi.

Ta kuma ce taɓo farashin fetur inda ta ce daga N87 a 2015 yanzu ana sayarwa kan N165.

  • Rashawa

PDC ta ce abin dariya ne gwamnatin APC ta yi iƙirarin cewa tana yaƙi da rashawa, bayan kuma ta zama matattarar ƴan siyasa masu kashi gindi. Jam’iyyar hamayyar ta kuma ce wannan ne ya sa APC ta gaza hukunta jami’ai da shugabanninta da ake tuhuma.

“Shi ya sa ba ta da amsa kan rahoton da ya bankaɗo yadda shugabannin APC suka wawuri naira tiriliyan 25 daga hukumomin gwamnati,” kamar yadda PDP ta yi iƙirari.

  • Ayyukan yi

Babbar jam’iyyar mai hamayya a Najeriya ta ce “abin takaici ne gwamnatin APC ta fito tana lissafa ayyukan more rayuwa a matsayin nasarori waɗanda a takarda kawai suke tare da ƙoƙarin aiwatar da ayyukan da gwamnatin PDP ta yi.

“PDP ta ƙalubalanci gwamnatin APC ta fito ta bayyana wani muhimmin aiki da ta tsara, ta fara ta kuma kammala a cikin shekaru shida da suka wuce,” in ji babbar jam’iyyar adawar.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement