Connect with us

News

‘Babu Bangaren Da Buhari Ya Dauka A Rikicin Siyasar Kano’

Published

on

Spread the love

Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani kan jawabin da bangare daya na Jam’iyyar APC a Jihar Kano ya yi cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da bangarensa. Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da fitar mai taken ‘Shugaba Buhari yana goyon bayan Jam’iyyar APC, ba bangare daya ba’.A

sanarwar, Malam Garba ya musanta batun cewa Shugaban yana goyon bayan bangare daya a cikin bangarorin jam’iyyar da suke rikici a Jihar Kano.

A cewarsa, “Wannan ba zai yiwu ba alhalin lamarin na gaban kotu.

Advertisement
  1. Bisa tabbaci, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba ya goyon bayan kowane bangare.“Goyon bayansa na Jam’iyyar APC ce dulkulalliya mai karfi, ba bangaranci ba.” Wata Kotun Abuja ce a ranar 30 ga Nuwamba ta yanke hukuncin cire shugabancin jam’iyyar na bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda ta ya ce tsagin bangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ne zababbun shugabannin APC na hakika.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply