Connect with us

News

Kuyi amfani da FCAPT wajen bunkasa noma – Farfesa Sharubutu

Published

on

Daga Muhammad zahraddin

 

 

Shugaban hukumar binciken noma ta (ARCN), Farfesa Garba Hamidu Sharubutu ya ja hankalin kwararru dake kwalejin horas da fasahar noma ta (FCAPT), da su sadaukar da kansu wajen cimma muradan kafa ta na bunkasa bangaren noma.

Farfesa Sharubutu ya bayyana hakan ne a taron kungiyar tsoffin daliban kwalejin karo na biyu da aka yi a Kano.

Sharubutu na cewa ya zama wajibi ga kwararrun su kawo sabbin dabarun fasahar noman zamani, yadda za a rage matsalolin noma da hanyoyin sarrafa amfanin aka girbe ba tare da ya lalace ba, da kuma alkinta shi.

Ya kara da cewa shakka babu Gwamnatin tarayya ta maida hankali wajen bunkasa kwalejin duba da muhimmancin da take da shi a tsakanin al’umma.

“Babban abin dubawa yadda zamu amfani wannan damar wajen ilmantar da manoma, bada horo don ganin noma ya bunkasa a dukkan matakai.

Sauya hanyoyin noma na lokacin kaka da kakanni a yanzu abu ne mai matukar fa’ida, musamman fito da iri masu yi da wuri, nau’ukan takin zamani da yadda ake sarrafa shi a kimiyyance.

Mun wuce lokacin da dole sai an yi noma a lokacin damina, kimiyya tazo da fasaha daban-daban da ya kamata mu sanar da manoman mu don wanzuwar ci gaba,” Farfesa Sharubutu.

Shugaban hukumar binciken noma ta kasa ya kuma bukaci kwararrun da malaman dake koyarwa a kwalejin da suyi amfani da damar da suke da ita wajen karo karatu, don fadada matakin fasahar su.

“Ilmi shi ne mabudin kowanne irin ci gaba, don haka nake kara kira da masu matakin karatu na digiri na biyu su yunkura don yin na uku, da wannan ne ci gaban da ake muradi zai tabbata a kwalejin FCAPT”.

Da yake amsa tambayoyi kan hatsaniyar da ta tashi watannin baya a kwalejin ta FCAPT, Farfesa Sharubutu ya alakanta matsalar da rashin samun cikakkun bayanai daga bangaren su, da kuma rashin fahimta tsakanin hukumar gudanarwar kwalejin da malaman dake koyarwa.

“Tuni muka samar da daidaito wajen tabbatar da cewa kowane bangare ya fahimci abinda ya kamace shi”.

Da yake bayani tun da fari, shugaban kwalejin horas da fasahar noma ta FCAPT, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram ya sha alwashin kawo ci gaban da ake muradi ta fuskar noma.

Dr. Gwaram ya kuma godewa tsoffin daliban da suka shirya taron, inda ya bukacesu ci gaba da wanzar da zumuncin dake tsakanin su.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement