Connect with us

News

Za mu rinka tura malaman mu zuwa Algeria domin neman ilimi – Ganduje

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a shirye Kano ta ke ta hada hannu da kasar Algeria, domin inganta ilimi a jihar.

Dr Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da hakan ne a lokacin da ya karbi bakwancin shugaban darikar Tijjaniyya na duniya, Ali Bel Arabi a fadar gwamantin Kano.

“Za kuma mu yi kokari wajen aiko malaman mu zuwa kasar Algeria, domin su rinka samun ilimi”. Inji Ganduje

Shi kuwa Sheikh Ali Abel Arabi, ya nuna jin dadin sa tare da godewa al’ummar Kano da Najeriya baki daya.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement