Connect with us

News

An kama mutumin da ya yi niyyar sayar da ɗansa don ya sayi babur

Published

on

Daga muhammad muhammad zahraddin

Ƴan sanda a Liberia sun kama wani mutum ɗan shekara 29 ɗan ƙasar Saliyo inda ake zarginsa da yunƙurin sayar da ɗansa mai shekara 10.

Bayan kama mutumin, ya shaida wa masu bincike a Monrovia babban birnin Liberia cewa ya yi niyyar sayar da ɗan nasa ne sakamakon yana neman kuɗi cikin gaggawa domin sayen sabon babur.

Ya bayyana cewa akwai babur ɗin abokinsa da ke hannunsa wanda aka sace, hakan ya zama tilas a gare shi ya nemi kuɗi da suka kai kimanin dala dubu ɗaya domin sayen sabo domin ya mayar wa abokinsa.

Ya shaida wa jami’ai cewa an ba shi shawarar cewa idan yana so ya samu kuɗi cikin gaggawa, hanya ɗaya da zai bi ita ce ya yi sauri ya je Liberia mai makwaftaka ya sayar da ɗansa.

Safarar bil adama babban al’amari ne a Yammacin Afrika.

Yaran da ake sayar da su domin aikin bauta akasari ba a barin su suna tuntuɓar iyayensu, ana tursasa su aiki a matsayin ma’aikatan gida ko kuma leburori.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement