Connect with us

News

Yara miliyan 3.6 za a yi wa rigakafin cutar Polio a Kano a watan Janairu – Ganduje

Published

on

Daga  Yasir sani Abdullah

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa yara miliyan 3.6, ƴan ƙasa da shekara 5 ne za a yi wa rigakafin cutar shan inna a gangamin Makon Haihuwa da kula da lafiyar Yara na watan Janairu.

A cewar sa, aikin gangamin za a gudanar da shi ne tare da jami’an kai daukin gaggawa yayin annoba, inda jami’an rigakafin za su bi gida-gida don yi wa yara ‘yan kasa da shekaru 5 rigakafin cutar shan inna.

“Manufar Makon Haihuwa da kula da Yara da Mata masu juna biyu shi ne inganta harkokin kiwon lafiya ga mata masu juna biyu da ‘ya’yansu.” Inji shi.

Cikin sanarwar da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin gwamna, Hassan Musa Fagge ya fitar, Gwamnan wanda mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya baiyana hakan a ranar Lahadi a Ƙaramar Hukumar Ungogo, yayin ƙaddamar da gangamin makon haihuwa da kula da yara da mata masu juna biyu a jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano ta himmatu sosai wajen samar da isassun kayan aikin kiwon lafiya ga al’ummarta saboda haka… “bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin mata masu juna biyu suna zuwa asibiti a fadin jihar”.

Gwamnan ya yabawa Gwamnatin Tarayya, Shugabannin Kananan Hukumomi, Masarautu da kuma masu bada tallafi a fannin kula da lafiya bisa jajircewar da suka yi na ganin an samu ci gaba mai ma’an, don haka ya bukace su da su kara kaimi kan nasarar da aka samu a aikin.

A nasa bangaren, kwamishinan lafiya na jihar Dr.Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bukaci iyaye su bada hadin kai ga jami’an rigakafi domin ganin an samu nasarar aikin.

Sauran masu ruwa da tsaki da suka yi jawabi a yayin bikin sun hada da wakilin Sarkin Kano, Dankadan Kano Dr. Bashir Muhammad, shugaban karamar hukumar Ungogo Alh.Abdullahi Garba Ramat da wakilan kungiyoyin bada tallafi.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement