Connect with us

News

Bola Tinubu: Manyan ƙalubalen da ke gaban tsohon gwamnan Lagos a zaben 2023

Published

on

Daga muhammad muhammad zahraddin

Matakin da jagoran jam’iyyar APC a Najeriya kuma tsohon gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ɗauka na bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023 wata alama ce da ke nuna cewa an buga kugen siyasa yayin da ake tunkarar zaɓe mai zuwa.

An daɗe ana raɗe-raɗin cewa Tinubu zai tsaya takarar shugaban ƙasa, sai dai ya furta hakan da bakinsa a fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ya gana da shi ranar Litinin.

Advertisement

Tinubu dai babban mai fada a ji ne a jam’iyyar APC, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen nasararta a zaɓukan 2015 da kuma 2019, kana ya samu damar kafa yaransa na siyasa da dama a wurare daban-daban waɗanda su ma a yanzu sun samu ƙarfin iko a jam’iyyar, wani abu da ake ganin zai taimaka masa.

Sai dai duk da waɗannan damarmaki da mutumin da ake kira Jagoran APC ke da su, wasu masana harkokin siyasa na ganin cewa akwai wasu manyan ƙalubale da ka iya yi masa tarnaƙi wajen cikar burin da ya shafe tsawon rayuwarsa yana fatan cikarsa, kamar yadda ya bayyana da bakinsa.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, wani masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana min cewa babban ƙalubalen da Tinubu zai fuskanta wajen neman tikiti da kuma shiga zaɓe idan ma ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyarsa shi ne na rashin lafiya.

Advertisement

A shekarar da ta gabata Tinubu ya kwashe watanni yana jinya a birnin Landan abun da ya sa mutane suka fara jefa ayar tambaya a kan lafiyarsa, da yake tun a wancan lokacin aka fara raɗe-raɗin zai tsaya takarar shugaban ƙasar. Sai dai ya sha cewa yana da kuzarin da zai iya shugabantar kasar, kuma magoya bayansa sun ce mahassada ne suke cewa ba shi da lafiya.

A cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge ”Idan a wasu wurare ne yadda yake fama da rashin lafiyar nan mutane ma ba za su dinga zancensa ba, kuma ko an neme shi shi zai ƙi amincewa, domin lafiya na da matuƙar muhimmanci wajen jagorancin babbar ƙasa irin Najeriya”

Shi ma Dakta Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Abuja, ya ce akwai ayar tambaya kan lafiyar Tinubu, musamman idan aka yi duba na tsanaki kan yadda yake al’amuransa.

Advertisement

Ya ce ”A halin da ake ciki mutane na ganin cewa samun mutum mai kuzari ya shugabanci Najeriya shi ne babban abun da ake buƙata, shi kuwa kaga abun da ya banna a zahiri shine ba shi da lafiya, to ka ga za a iya rasa wannan kenan.

”An yi wasu shugabanni a baya a Najeriya da suka yi fama da rashin lafiya, kuma an ga yadda hakan ya kawo tsaiko a harkar gudanar da gwamnati, shi Tinubu kowa ya san yana fama da rashin lafiya ko da yake ba ka iya cewa ga cutar da yake fama da ita, amma a fili take cewa idan aka sake maimaita abun da aka yi a baya hakan zai zama kuskure” a cewarsa.

Wani babban ƙalubale da Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce Tinubu zai iya fuskanta a 2023 shi ne gwamnonin jam’iyyar APC da ke da buƙata irin tasa, ko kuma wacce ba ta kai tasa ba a zaɓen na 2023.

Advertisement

”Wasu daga cikinsu na neman samun kujerar mataimakin shugaban ƙasa, wasu shugabancin jam’iyya wasu kuma kujerar shugaban ƙasar ma suke nema, kuma suna ganin cewa sanya Tinubu a gaba zai iya daƙile cikar nasu burinsu” in ji shi.

Dakta Abubakar Kari kuwa cewa ya yi wasu daga cikin waɗannan gwamnoni da ke fatan zama mataimakin shugaban ƙasa na ganin cewa idan Tinubu zai yi wa APC takara to yawancinsu ba zai yiwu su samu wannan kujera ba, domin a matsayinsa na Musulmi ana sa ran zai ɗauko Kirista ne domin yi masa mataimaki, don haka tunda su musulmai ne zai yi wuya su samu wannan dama, saboda zai yi wuya a haɗa musulmi da musulmi su yi takara.

“Ko a yankinsa na kudu maso yamma ma ba za ka iya cewa dukkan gwamnonin na goyon bayansa ba, biyu daga ciki ne za ka iya cewa suna goyon bayansa, gwamnan Osun wanda ɗan uwansa ne, da kuma gwamnan Legas wanda shi ya kawo shi,” a cewar Dakta Kari.

Advertisement

Kazalika Dakta Kari ya kara da cewa mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo zai iya zame wa Tinubu ƙashin-wuya, domin a fili take cewa akwai wasu makusantan Shugaba Muhammadu Buhari waɗanda ba sa son Tinubo, don haka abu ne mai wuya su amince da shi.

”Wasu na ganin cewa sai lallai kana da tsari, sannan ka kafu a siyasance za ka iya zama shugaban ƙasa, amma a zahiri mun san cewa ko Jonathan lokacin da ya zama shugaban ƙasa ba shi da wani tsari na siyasa, sannan bai yi kafuwar da za ka ce ita ce ta sa ya ci zaɓe ba, don haka babu abun da zai sa hakan ya yi tasiri a kan Osinbajo a yanzu” a cewar Kari.

Wani babban ƙalubale da shi ma ka iya kawo wa Tinubi cikas ko da ya samu tikitin yi wa APC takara a zaɓen 2023 shi ne zargin da wasu suke yi na rashin cika alkawuran da jam’iyyar APC mai mulki ta yi bayan nasarar da ta samu a 2015.

Advertisement

APC dai ta yi wa ƴan Najeriya alƙawura da dama, musamman daƙile matsalar tsaro, da yaki da cin hanci da rashawa da kuma farfaɗo da tattalin arziƙi, sai dai wasu na da ra’ayin cewa babu wani daga cikin waɗannan alƙawura da jam’iyyar ta cika.

“An samu matsaloli da dama, yawancin abubuwan ta yi alkawarin za ta yi ba ta yi ba, ga talauci ga tsadar kaya ga rashin aikin yi, kuma shi Tinubu yana cikin waɗanda suka sayar da jam’iyyar nan a wajen ƴan Najeriya, don haka yana ɗaya daga cikin waɗanda ake ɗorawa alhakin gazawar jam’iyyar a wannan lokaci,” a cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Bola Tinubu mutum ne wanda ake ta ruɗani a kan shin wane ne ma shi, akwai tababa a kan daga ina ya fito, ɗan wacce jiha ne shi?, shin shekarunsa nawa?, kai hatta iyalinsa da takardun karatun da ya yi da sahihancinsu da inda ya yi su, da kuma hanyar da ya bi ya tara kuɗin da yake da su” in ji Dakta Abubakar Kari.

Advertisement

Ya ƙara da cewa waɗannan tambayoyi ne masu muhimmanci waɗanda har yanzu yake zille musu, kuma matsawar jama’a ba su samu amsarsu ba to lallai zai iya fuskantar ƙalubale a kansu.

Shi ma Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce har yanzu mutane sun kasa fahimtar abubuwa da dama a kan Tinubu musamman yadda ya tara dukiyarsa, kuma dukkan waɗannan abubuwa ne da za su bijiro a nan gaba.

”Bai taɓa ba da amsoshin waɗannan tambayoyi ba, wataƙila ko don ba ya son ya amsa ne ko kuma saboda wani dalili da mutane ba su sani ba,” in ji shi.

Advertisement

Jihar Kano da ke arewa maso yamamcin Najeriya ce ta fi yawan ƙuri’u a duk lokacin da aka zo zaɓe, don haka tana da matuƙar tasiri wajen samun nasara, shi ya sa masu neman zama shugaban ƙasa a Najeriya suke ƙwallafa ransu a kan Kano don ganin sun samu waɗannan ƙuri’u.

Ko da yake wasu na ganin tuni Tinubu ya fara yaɗa manufofinsa a jihar ta Kano, Dakta Abubakar Kari ya hango masa cewa yana da babbar matsala a jihar saboda mutane na kallonsa a matsayin wanda ya taimaka wajen murɗe zaɓen jihar na 2019 da ake zargin an yi.

”Yawancin waɗanda ke goyon bayan abun da aka yi shi suke ɗora wa laifi, kuma su kansu masu faɗa a ji waɗanda da suna nan da yawa a Kano da kuma ƴan Kwankwasiyya za su yaƙi nasararsa idan ma ta tabbata cewa shi zai yi wa APC takara”.

Advertisement

Tuni dai wasu jami’an gwamnatin Kano suka fara nuna goyon bayansu musamman a shafukan sada zumunta, wata ƴar manuniya da ke nuna inda aka sanya gaba.

Baya ga haka gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na cikin waɗanda ake ganin cewa zai zame wa Tunubi mataimaki idan dai ta tabbata cewa ya zaɓi ya ɗauki musulmi a matsayin mataimakinsa.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *