Connect with us

News

EFCC ta cafke lauyan bogi kan amfani da jabun takardu da yin sojan-gona

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC, ta cafke wani lauyan bogi, Adekola Adekeye, bisa amfani da jabun takardu domin ya yi damfara.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis, ya ce asirin Adekeye ya tonu ne lokacin da ya zo ofishin hukumar na Jihar Legas domin karɓar belin wani ɗan damfara.

“Wanda a ke zargin, ya je ofishin mu na Legas a ranar 11 ga watan Janairu, inda ya nuna kan sa a matsayin lauya, domin ya karɓi belin wani ɗan damfara da ke tsare a ofishin na mu na Legas.

Advertisement

“Amma sai asirin Adekeye ya tonu bayan da jami’an mu su ka tsananta bincike domin gano gaskiyar takardun da ya nuna musu domin karɓar wannan na tsaren.

“Da bincike ya kai mu gidan sa, sai mu ka gano takardun bogi da dama da kwanan watan su tun 2005 , har da jabun takardun Jami’ar Legas ta jiha da na Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara.

“Ya kuma yi ƙaryar cewa shine mai chambar lauyoyi mai suna “A.A. Emmanuel & Co. Chambers,”, inda da kamfanin ya ke amfani ya yi damfara kafin a cafke shi.

Advertisement

“Nan ba da daɗewa ba za mu kai shi kotu,” in ji Uwujaren.

Ya ci alwashin cewa hukumar za ta ci gaba da zaƙulo irin wadannan ƴan damfarar da su ke amfani da jabun takardu domin karɓar belin masu laifi, i. Da ya tabbatar da cewa hukumar za ta hukunta duk wanda a ka kama.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *