Connect with us

Sport

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Mbappe, Vlahovic, Christensen, Henderson, Carroll

Published

on

 muhammad muhammad zahraddin ( INDARANKA )

Ɗan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe na tattaunawa da ƙungiyarsa ta Paris St-Germain. Tun farko an sa ran dan wasan mai shekara 23 zai koma Real Madrid ne a kyauta a ƙarshen wannan kakar wasan. (Daily Telegraph – subscription required)

Fiorentina ta kusa amincewa da tayin fam miliyan 58.4 da Arsenal ta yi kan dan wasan gaba Dusan Vlahovic mai shekatra 21. (La Repubblica – in Italian)

Advertisement

Bayern Munich da Barcelona na son daukan dan wasan baya na Denmark Andreas Christensen mai shekara 25 da zarar kwantiraginsa ta kare a Chelsea a karshen wannan kakar wasan. (Fabrizio Romano, on Twitter)

Manchester United ta tuntubi kocin Inter Milan Simone Inzaghi domin sanin ko zai karbi ragamar kungiyar a karshen wannan kakar wasan, inda dan kasar Italiyan zai fara wani aji na koyon turanchin Ingilishi a cikin shirin kama aiki a Old Trafford. (Corriere Dello Sport – in Italian) 

Southhampton ta nemi Manchester United ta sanar da ita ko golanta Dean Henderson na kasuwa a cikin wannan watan na Janairu. (Football Insider)

Advertisement

Arsenal ta yi nisa a tattaunawar da ta ke yi da Juventus kan aukan aron dan wasan tsakiya Arthur Melo mai shekara 25 na tsawon wata shida. (Daily Telegraph – subscription required)

Burnley kuwa ta mayar da hankali ne kan daukan Andy Carroll, tsohon dan wasan gaba na Newcastle da Liverpool. Dan wasan mai shekara 33 zai kasance ba bu wata kwantiragi a kansa a karshen wannan wata na Janairu. (Daily Mail)

Tottenham ta yi wa Wolves tayin ba ta ƴan wasanta hudu idan ta amince ta ba ta Adama Traore, dan wasan gefe dan Sfaniya mai shekara 25. (Teamtalk)

Advertisement

Barcelona na iya sayar da Sergino Dest a wannan watan na Janairu domin samin kudin sayo wani sabon dan wasan gaba, inda Chelsea da Bayern Munich suka nuna sha’awarsu kan Ba’amurken dan wasan mai shekara 21. (ESPN)

Flamengo ta yi wa Manchester United tayin fam miliyan 8 domin ta sayar ma ta da dan wasan tsakiya Andreas Pereira wanda dama yana zaman dan aro ne. (Sun)

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *