Connect with us

News

Yadda wani yaro ya yi wa ‘yar maƙocinsa yankan rago

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

A kullum ayyukan ta’addanci sai ƙaruwa suke yi a jihohin Arewacin Najeriya, irin ayyukan ta’addancin da da can ba a san su ba, kuma ba a ma tunanin yiwuwar faruwar su, amma a yau sai ga shi irin waɗannan munanan laifuka suna nema su zama tamkar ruwan dare, a sakamakon yadda matasa suke ta’ammuli da ƙwayoyi da kallace-kallacen muggan fina-finai da suke kiyar da ta’addanci da baɗala a zahiri. Wasu daga cikin irin waɗannan fina-finan ma da harshen Hausa ake gabatar da su.

Kafar BBC ta rawaito labarin inda wani yaro matashi, wanda yake da ƙananan shekaru ya aikata kisan gilla ga ‘yar maƙocinsa, ya kashe ta har lahira ba tare da wani gezau ba.

Majiyar TDR Hausa ta bayyana cewa “Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mazaunin Ƙaramar Hukumar Tofa da ke jihar bisa zargin yin garkuwa da wata yarinya mai suna Zuwaira Gambo kuma ya yanka ta a garin Sabon Fegi a dai garin Tofa.

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu gawar yarinyar mai shekara 13 ne a wani kango da ke garin Tofa, kwana guda da ɓatan ta.

Haka zalika ta ce ta kama matashin ne bayan sama da kwanaki dari biyu da faruwar al’amarin, a lokacin da yake shirin karbar kudin fansar kanin marigayiyar.

Matashin dai mai suna Auwwalu Abdulrashid, wanda ake wa laƙabi da Lauje, yana makwabtaka da gidansu wadda ake zarginsa da kashewa, kamar yadda mai magana da yawun rundundar ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana.

Advertisement

Tun bayan da ya yi garkuwa da yarinyar, ya buƙaci a ba shi naira miliyan guda a matsayin kuɗin fansa, amma bayan an yi ciniki an tsaya kan dubu 400. Amma ana tsaka da cinikin kawai sai aka ga gawarta an yar da ita a wani kango.

Shi ma mahaifin yarinyar cikin kuka ya yi wa BBC bayanai kan yadda ya samu gawar yarinyarsa inda ya ce yana dab da zuwa biyan kuɗin fansar ƴarsa ya samu labarin an kashe ta inda ya tarar da ita an yanke mata maƙogwaro sa’annan an rufe mata baki.

A cewar Kiyawa, bayan binciken da suka yi, wanda suka kama ya tabbatar musu da cewa shi ya kashe Zuwaira, a cewarsa “ya yaudare ta, ya kai ta kango, sannan kuma ya ɗauki hijabinta ya shaƙe mata wuya ya ɗauko wuƙarsa ya yanka ta.”

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa daga nan ne wanda ake zargin ya ɗauki fatanyarsa ya haƙa rami sannan ya binne ta a wani kango da ke kusa da gidansu.

A cewar Kiyawa, sai bayan kwanaki sama da 200 da faruwar wannan lamarin asirin wanda ake zargin ya tonu bayan wanda ake zargin ya yi garkuwa da ƙanin marigayiyar mai suna Muttaƙa inda ya nemi a ba shi naira miliyan biyu.

Daga baya sai aka ba shi naira dubu 100 ya saki yaron, inda aka ɗauko yaron a wata makarantar firamare da ke Dawanau a Kano.

Advertisement

Duka wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu da ake zargin masu satar mutane ne suka sace mahaifiyar shugaban marasa rinjaye na majalisar dokoki ta Kano, Honourable Isyaku Ali Danja a tsakar daren Talata.

Maharan sun shiga gidan Hajiya Zainab da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa, ɗauke da makamai, inda suka tafi da ita.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, sai dai lamarin bai yi ƙamari a Kano ba kamar jihohi maƙotanta.”

Advertisement

Irin wannan lamari na rashin imani yana cigaba da faruwa a jihar Kano, wanda ya kamata jama’a su sa ido game da yadda ‘ya’yansu suke watangaririya a gari, ba tare da lura ba.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply