Connect with us

News

Buhari ya ba mu kunya – Dattawan Arewa

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Ƙungiyar dattawan Arewacin Naeriya (NEF), ta ce shugaba Muhammadu Buhari abin takaici ne ga arewa.

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna ranar Asabar, mai magana da awun ƙungiyar Hakem Baba-Ahmed ya ce Buhari ya yi alkawarin tabbatar da tsaro da kuma bunkasa tattalin arzikin amma ya kasa yin hakan.

Ya shawarci ƴan Arewa su zaɓi cancanta a zaɓen 2023.

“An gaya wa ’yan Arewa cewa idan Buhari ya zama shugaban ƙasa za a shawo kan matsalolinsu amma komai ya sake taɓarɓarewa a ƙarƙashin mulkina, wannan ba farfaganda ba ce; ba almara ba ce, abu ne a zahiri” in ji shi..

Ya ƙara da cewa “Akwai miliyoyin ƴan gudun hijira a yankin arewa inda Buhari ya fito sakamakon munanan ayyukan ƴan bindiga, amma gwamnati ta ƙi amincewa da hakan, wannan ba ita ce Najeriyar da muka zaɓa a ƙarƙashin Shugaba Buhari

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement