Connect with us

News

Gwamnatin Nijeriya za ta kashe naira biliyan 1.4 ga matasan manoma

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Majalisar Zartaswa ta sahale da a kashe naira biliyan 1.4 domin samar da kayan aikin gona da kuma iri domin Shirin Noman Matasa na Ƙasa.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu na Ƙasa, Lai Mohammed ne ya baiyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa a jiya Laraba a Abuja.

Ya ce an bada kwangiloli huɗu domin fara shirin, in da ya nuna ƙwarin gwiwa cewa shirin zai zaburar da matasa su shiga sana’ar noma.

Advertisement

A cewar sa, kwangilar farko ita ce kawo kayan yin noma da su ka haɗa da iri, auduga, kayan shuka, magungunan kwari, taki da sinadarin saka shuka girma ga gonaki masu girman kadada 3000 a jihohin Abia, Adamawa, Borno, Ekiti, Gombe, Imo, Jigawa, Katsina, Kebbi, Niger, Osun, Yobe da Enugu.

Ya ƙara da cewa kwangilar farko an kashe naira miliyan 313 a tsawon makonni biyu.

Mohammed ya ƙara da cewa kwangila ta biyu itace samar da injina da motocin noma a wasu zaɓaɓɓun jihohi da su ka haɗa da Kaduna, Katsina, Kebbi, Osun da Jigawa.

Advertisement

Ya ce ta uku it ace samar da injinan gyaran gona a wasu zaɓaɓɓun jihohi da su ka haɗa da Kaduna, Katsina, Kebbi, Osun, Jigawa ds Gombe.

Inda ya ƙara da cewa kai kayayyaki da injinan noman zuwa jihohin Abia, Ogun, Ekiti, Katsina da Ebonyi zai laƙume Naira miliyan 2.5.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *