Connect with us

News

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano ta rufe makarantar da wanda yai garkuwa da Hanifah ya binne ta

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

Gwamnatin Nijar Kano ta bada umarnin rufe Noble Kids Academy, makarantar kuɗi da ke Kwanar Dakata, inda a nan ne Abdulmalik Tanko, wanda ya yi garkuwa da Hanifah Abubakar, ƴar shekara 5, ya kashe ya kuma binne ta.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa a jiya da daddare ne dai dubun Tanko ta cika, wanda shine malamin Hanifah a makarantar, amma ya sace ta ya kuma hallaka ta bayan ya karɓi wani kaso na naira miliyan 6 da ya nema a matsayin kuɗin fansa.

Da ya ke sanar da rufe makarantar na gaggawa a yau Alhamis, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammad Sa’idu Ƙiru, ya ce za a rufe makarantar ne bayan ƴan sanda sun gano gawar yarinyar a makarantar.

Advertisement

Da ya ke nuna takaici a kan lamarin a wata sanarwa da ya fitar, Ƙiru ya ce gwamnati za ta fara tantance makarantu mau zaman kan su domin a fito da wadanda basu da rijista domin magance aiyukan ɓatagari.

Ya kuma yi kira ga iyayen daliban makarantar Noble Kids Academy din da su tsaya da kai ya’yan su har sai an kammala bincike.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *