Connect with us

News

Hanifah: Ganduje ya sha alwashin tabbatar da adalci ga ɗalibar da malaminta ya kashe a Kano

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da “sa ido sosai” tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu a sace da kuma kashe Hanifah Abubakar.

A watan Disambar shekarar da ta gabata ne malamin Hanifah ƴar shekara 5, Abdulmalik Tanko ya yi garkuwa da ita, daga bisani ya kashe ta kuma ya binne gawar a makarantarsa ​​mai zaman kanta mai suna Noble Kids Academy da ke Kwanar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jihar.

Daga bisani ne dai jami’an tsaro su ka kama Tanko a ranar Laraba bayan da ya nemi a biya shi cikon Naira miliyan 6 da ya nema a matsayin kudin fansa.

Advertisement

Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya fitar a yammacin ranar Juma’a, gwamnan ya ce tuni aka dauki matakai kan lamarin da suka hada da rufewa tare da karɓe lasisin gudanar da makarantar da aka yi zargin cewa a nan ne a ka yiwa Hanifah kisan gilla.

Ya ce gwamnati ta damu matuka yadda mutanen da aka damka wa amana da kulawar yara kawai su zama masu kashe su.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa gwamnati ta tuntubi iyalan marigayiyar kuma za ta ci gaba da tuntuɓar su har sai an tabbatar da adalci a shari’ar don ya zama izina ga wasu.

Advertisement

Gwamnan wanda ya yabawa jami’an tsaro a jihar kan daukar matakin da suka kai ga cafke wadanda ake zargi da hannu a lamarin, ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, gwamnati za ta bi diddigin lamarin har ta kai ga gaci.

Ya kuma yabawa kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma ‘yan Najeriya masu kishin kasa da suka nuna damuwa da lamarin.

Gwamna Ganduje ya kuma ba da tabbacin goyon bayan hukumomin tsaro na gwamnati wajen gudanar da ayyukansu na ganin cewa Kano ta samu zaman lafiya.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *