Connect with us

News

Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda 2 sun kuma tafi da wani ɗan kasuwa a Jigawa

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

 

Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta ce wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe jami’an ta biyu tare da yin garkuwa da mutum daya a Ƙaramar Hukumar Taura.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Dutse ranar Litinin.

Advertisement

Shiisu ya ce lamarin ya faru ne bayan da ‘yan bindigar suka kai farmaki gidan wani Ma’aru Abubakar da ke garin Kawalam, inda su ka yi awon gaba da shi.

“A ranar 23/01/2022, da misalin karfe 1:30 na dare, mun samu kiran kar-ta-kwana cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari garin Kwalam da ke Ƙaramar Hukumar Taura.

“Bayan samun rahoton, nan da nan mu ka haɗa tawogar ‘yan sanda muka nufi wurin da lamarin ya faru. Da isowar mu mu ka riƙa yin batakashi da su har su ka tsere.

Advertisement

“Sai dai kuma sun samu nasarar harbe ASP Anas Usaini da Sunusi Alhassan a kusa da wata motar sintiri da ‘yan bindigar suka kona.

“Bincike na farko ya nuna cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Alhaji Ma’aru Abubakar mai shekaru 60 a garin Kwalam inda suka yi awon gaba da shi,” in ji Shiisu.

Ya kuma baiyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an kubutar da wanda su ka yi garkuwa da shi, tare da cafke ƴan bindigar da su ka tafi da shi.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *