Connect with us

News

Bankin duniya ya bawa gwamnatin tarayya naira tiriliyan 311 ta rabawa talakawan Najeriya

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

A yunƙurin shirin na bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, gwamnatin tarayya ta fito da wani sabon shiri mai suna NG-CASES wanda da za a aiwatar da bashin bankin duniya har naira tiriliyan 311,250.

Mataimakin shugaban ƙasa, farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin a ranar Alhamis 20 ga watan Janairu, 2022 a babban birnin tarayya Abuja.

Wani rahoto daga Nairametrics ya bayyana cewa shirin na NG-CARES, shiri ne wanda ya ke da ɓangarori da dama.

Advertisement

Shirin zai cigaba da gudana tare da sauran shirye-shiryen rage raɗaɗin talauci na gwamnatin tarayya da ke gudana a ƙasar.

A cewar farfesa Osinbajo, shirin an yi shi ne domin talakawan ƙasar.

Abinda shirin shugaba Buhari ya ƙunsa

Advertisement

Ya bayyana cewa shirin NG-CARES an tsara shi ne domin tallafawa talakawa, bayar da agajin gaggawa ga ƙananun manoma da masu ƙananun sana’o’i waɗanda annobar cutar korona ta shafa. Ya ƙara da cewa shirin an kafa shi ne akan hanyoyin da ƙasar ta ke bi domin ɗaƙile raɗaɗin da annobar korona ta kawo wa mutane.

Abinda Osinbajo yace

Osinbajo ya ce, bashin na bankin duniya zai shafe tsawon shekaru biyu (2021-2023), kowace jiha za a bata biliyan N8.2, a hasashen da aka yi, babban birnin tarayya Abuja zai samu biliyan N6.2 sannan kowane ɓangaren taimako na shirin NG-CARES zai samu biliyan N6.2.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *