Connect with us

News

Gwamnatin Buhari ta Fi ta Kasar Amurka Aiki -Fashola

Published

on

Daga Yasir sani abdullahi

 

 

Ministan Aikace-Aikace da Muhalli Babatunde Fashola yace gwamnatin Shugaba Buhari ta fi gwamnatin Amurka yin aiki.

Fashola ya fadi hakane a Jahar Kano a yau Alhamis a yayin taron Jam’iyyar APC.

Taron ya kunshi tattauna akan nasarar da jam’iyyar APC ta samu a shekaru 7 da tayi tana mulkin Nigeriya.

Fashola wanda shine tsoho gwamnan Jahar Lagos yace “Ina tabbatar muku mulkin APC na Shugaba Buhari yayi nasarar da gwamnatin Amurka bata yi shi ba, A watan Disamba shekarar 2021 mun kammala hanyoyin masu kilomita 941 a tsakanin Jahohin kasar nan.

“Misali a Jahar Kano akwai aikin Hanya 21 a ciki da wajen Jahar da ma kauyikan da suke makwabtaka.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement