Connect with us

Sport

Aubameyang na daf da sauya sheƙa zuwa Barcelona

Published

on

Aubameyang na daf da sauya sheƙa zuwa Barcelona

Yayin da saura ƙasa da awanni biyu a rufe kasuwar cinikaiyar ƴan wasa ta tsakiyar kaka, da alama dai fitaccen ɗan wasan gaban Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang na daf da sauya sheƙa zuwa Barcelona da ke Spain.

Tun a makon da ya gabata ne dai Arsenal da Barcelona su ke tattaunawa a kan ɗan wasan gaban, ɗan ƙasar Gabon.

Advertisement

A yau Litinin da safe tattaunawar sauya shekar Aubameyang ɗin ta ci tira, yayin da kungiyoyin ƙwallon ƙafar su ka kasa cimma matsaya a kan albashi ɗan wasan wanda ya kai fan dubu 340 a sati.

Kwatsam sai kuma ƙungiyoyi biyun su ka cimma matsaya inda Aubameyang, ɗan shekara 32 da haihuwa, zai sauya sheƙa zuwa Barca, wacce ta lashe Gasar Zakarun Turai 5.

Aubameyang dai zai koma Barca ne na dindindin.

Advertisement

Jaridar indaranka ta rawaito cewa a yayin kammala wannan rahoto, saura awa ɗaya da minti 33 a rufe kasuwar cinikaiyar ƴan wasan.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *