Connect with us

News

Matsalar tsaro: Mazauna Birnin Gwari na biyan miliyoyin naira ga ‘yan fashin daji, El-Rufa’i ya roƙi a kawo musu ɗauki

Published

on

Spread the love

Daga 

muhammad zahraddin

Bayanai daga ƙaramar hukumar Birnin Gwari, mai fama da hare-haren ‘ya fashin daji sun ce a baya-bayan nan wasu ƙauyuka a yankin sun biya kimanin naira miliyan 45, a matsayin sulhu da ‘yan fashin daji.

Advertisement

Ƙauyukan su fiye da goma a mazaɓar Magajin Gari ta 2 sun biya kuɗaɗen ne bayan ‘yan fashin dajin da ke yankin, sun nemi lallai su biya wannan diyya, matuƙar suna son zaman lafiya.

Birnin Gwari a Kaduna, na cikin yankunan da suka fi fama da taɓarɓarewar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya.

Bayanai sun ce wani hari da ‘yan fashin daji suka kai ƙauyen Awaro kimanin mako uku a baya ne, ya ƙara tsorata mutanen yankin har suka miƙa wuya. Wani shaida ya ce sun yi amfani da harin wanda aka kashe mutum ɗaya a matsayin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

Advertisement

Ya ce, “sun shaida mana cewa wannan somin-taɓi ne kuma su basa ma son batun sulhu, wannan dalili ya sanya mutane shiga gudun hijira. Garin da suka je suka diba mata a gidan biki na cikin manyan garuruwa”.

Shi ma wani mai tattara bayanai kan hare-haren ‘yan fashi a yankin ya faɗa wa BBC cewa ƙauyukan goma sha uku na cikin al’ummomin da suka tsallake harajin ‘yan fashi a damunar da ta wuce.

Amma kuma a baya-bayanan sun gargaɗe su da cewa ko dai su biya su zauna lafiya a yanzu, ko kuma su yi noma a damuna mai zuwa, ko kuma su ci gaba da fuskantar hare-hare.

Advertisement

“Sai da kowanne magidanci ya biya kudin, har da wadanda suke hijira, ko da hali ko ba hali, wasu ma ranta musu aka yi suka biya. Ƙauyuka 14 ne suka hada kudin.” Ya kuma kara da cewa an biya kudin ne a satin da ya gabata.

Shi ma wani shaida da ya ce ya ga kuɗin da idonsa, ya shaidawa BBC cewa; “Wasu na cewa miliyan 45 amma akwai yiwuwar yafi haka, a buhunan taki aka zuba kudin, akwai wadanda suka biya dubu 100 wasu kuma dubu 200”.

Zaman ɗar-ɗar

Rahotanni sun ce zuwa yanzu ƙauyukan da suka biya wannan haraji, ba su fuskanci wani sabon hari ba. Sai dai fargaba da zaman ɗar-ɗar sun dabaibaye zukatansu saboda rashin tabbas.

Advertisement

Da yawan waɗanda suka tafi gudun hijira zuwa garuruwa kamar Birnin Gwari, sun kasa komawa gidajensu a jihar ta Kaduna. Wadda mahukunta ke cewa ayyukan ‘yan fashin daji sun ƙaru a shekarar da ta wuce.

Halin da ake ciki a Kaduna da sauran yankunan arewa maso yamma mai fama da matsalolin tsaro ya tilastawa gwamnan Nasir El-Rufa’i neman ɗauki daga gwamnatin tarayya.

Gwamnan ya yi kira da aka kafa wata Babbar Cibiyar Ayyukan Soja (wato Theater Command) kan yaƙi da ‘yan fashin daji a yankin arewa maso yamma, kamar yadda ake da mai yaƙi da Boko Haram a Maiduguri.

Advertisement

Malam Nasir El-rufa’i na wannan kira ne jim kaɗan da karɓar rahoton tsaro na shekarar da ta wuce jihar sa ta Kaduna.

Gwamnan ya koka da cewa a bara kawai an kashe mutum 1,129, tare da sace shanu kimanin dubu 13, yayin da adadin mutanen aka sace ya kai ƙiyasin mutum 9 a kullum.

Ya ce masifar garkuwa da mutane da kashe-kashe karuwa yake ba raguwa ba, kuma babu tabbas wannan yanayi na sake daga musu hankali.

Advertisement

“Akwai bukatar ƙaro makamai da jami’an tsaro, saboda wanda ake da su yanzu sun yi kadan. Abin da ke faruwa shi ne idan an yaƙe su a wani yanki ko karamar hukuma sai su sauya sheƙa su koma wani wurin.”

El-Rufa’i ya ce dole idan za a taba Zamfara a yi tsari da zai hana ‘yan bindiga ratsawa ko iya kutsawa wata jiha makwabciya.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply