Connect with us

News

Hukumar WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 262,803

Published

on

Dakibai na rubuta jarrabawar kammala  sakandare ta 2023 ta WEAC

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Hukumar shirya jarrabawar ƙasashen yammacin Afrika (WAEC) ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 262,803 da suka rubuta jarrabawar kammala  sakandare ta 2023.

Shugaban ofishin hukumar a Legas, Patrick Areghan, ya ce an rike sakamakon jarrabawar ne bayan samun dalibai da tafka maguɗi a matakai daban-daban na jarabawar.

Kasar nan Ce Kan Gaba A Bangaren Masu Zaman Kashe Wando A Duniya

Ya ce kashi 16.29 na jimillar ɗaliban da suka rubuta jarrabawar ne lamarin ya shafa.
Mista Areghan ya yi bayanin cewa “dailan samun irin wannan matsala a bayyane suke, ɗalibai ba su zage damtse suka yi karatu ba, inda suka dogara da satar amsa a yayin jarrabawa.”

Bbc Hausa ta rawaito cewa ɗaliban da lamarin ya shafa suna da zaɓin gabatar da kansu don bincike da kuma neman damar wanke kansu daga wannan zargi na tafka maguɗin jarabawar, kamar yadda aka saba yi a baya.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement