Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Hukunta Wani babban sakatare Kan Zargin Badaƙala

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA.

 

Gwamnatin jihar Kano ta amince da gaggauta sauya babban sakatare na hukumar kula da ma’aikata, Mustapha Safiyanu Kabuga bisa zargin Badaƙala ajan sanya hannu kan takardun nadin mukamai a ma’aikatan jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun babban sakataren gwamnatin jiha Kabiru Sa’idu Magami a madadin sakataren gwamnatin jiha Dr. Baffa Bichi.

Tsohon Dan Jarida Mato Adamu ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.

Wata sanarwa da kwamishinan ya rabawa manema labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya fitar a ranar Asabar, ta ce, gwamnati ta kafa kwamitin tantancewa na mutane uku a karkashin jagorancin mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin ma’aikata, Dakta Sulaiman Wali. Sani ya binciki lamarin sannan ya mika rahotonsa cikin kwanaki goma.
Sanarwar ta ce, ”An sake mayar da famanan sakataren zuwa ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati har sai an kammala aikin kwamitin.

“Hakazalika, an nada Salahuddern Isa Habib a matsayin babban sakataren dindindin na hukumar daga ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, 2023.”

‘’Kwamitin yana da hurumin tantancewa da raba takardun karin mukamai na ma’aikatan jihar, wadanda wasu ma’aikatan hukumomi suka rubuta; da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga gwamnati bisa ka’idojin da suka dace.’’ in ji sanarwar.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement