Connect with us

Business

CBN Ya Sha Alwashin Farfado Da Darajar Naira A Kasuwar Canji

Published

on

Babban Bankin Najeriya CBN

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Babban Bankin Najeriya CBN ya sha alwashin bullo da sabbin matakai don magance faduwar darajar naira a kasuwar sauyin kudi.

Matakin na zuwa ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da Mukaddashin Gwamnan CBN, Folashodun Shonubi a jiya Litinin.

Ruwan Sama Ya Karya Gadar Da Ta Hada Bauchi Da Gombe

Da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, Mista Shonubi ya ce Tinubu ya bayyana damuwa kan halin da kudin kasar ke ciki a kasuwar canji ta duniya, lamarin da ya ce zai yi aiki don magancewa.

“Shugaban Kasa ya damu sosai da abubuwan da ke faruwa a kasuwar canjin, ya nuna damuwa game da rayuwar talaka,” in ji shi.

Ya jaddada yakinin cewa nan da ’yan kwanaki masu zuwa za a ga kyakkyawan sauyi dangane da matakan da aka dauka.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement