Connect with us

News

Sukar Ayyukan Ganduje Na Iya Kasancewa Cikin Dalilan Tinubu Na Hana Kwankwaso Minista – APC

Published

on

Kwankwaso, Tinubu, Ganduje

DAGA MARYAM BASHIR MUSA.

Jam’iyyar APC mai mulki ta ce akwai yiwuwar sukar da ake ci gaba da yiwa ayyukan shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje tsohon gwamnan jihar Kano, na cikin dalilan da suka sanya dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya rasa mukami a majalisar ministocin shugaba Bola Ahmad Tinubu.

Gabanin kaddamar da wadanda Tinubu ya nada a matsayin ministoci, akwai rahotanni da ke cewa Kwankwaso zai iya samun mukami a gwamnatin Tinubu, ganin irin alaka da ke tsakaninsu bayan zaben shugaban kasa.

Advertisement

Farashin Man Fetur Zai Ci Gaba Da Hauhawa — IPMAN

Sai dai Kwankwaso bai samu shiga jerin sunayen wadanda Tinubu ya nada a matsayin ministoci ba, yayin da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike na jam’iyyar adawa ta PDP, ya samu gurbi.

Da yake magana da manema labarai a karshen mako, daraktan yada labarai na Jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya ce ya yi amanna sukar da gwamna Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP da kuma ubangidan siyasar Kwankwaso ke yiwa Ganduje a jihar Kano, na cikin dalilan da suka sanya Tinubu ya yanke shawarar kin bai wa Kwankwaso mukamin minista.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *