Connect with us

News

Ƴan bindiga na shirin kai hari kan Jirgin ƙasan Kaduna-Abuja nan ba da jimawa ba” ~ DSS

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Wasu bayanan sirri da Jami’an farin kaya DSS suka fitar sun bayyana cewa ƴan bindiga na shirin sake kai ma Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari nan ba da jimawa ba.

Advertisement

Hukumar DSS a cikin wata sanarwa da suka aikewa Daraktan da ke kula da hukumar jiragen ƙasa ta ƙasa ta yi gargadi game da shirin kai hari da ‘yan bindiga suka shirya kai wa a kowane lokaci daga yanzu.

Tinubu ya sanar da ranar da zai rantsar da sabbin ministoci.

Haka kuma Takardar ta yi jan hankali akan Jami’an da ke kula da Jirgin gami da jami’an Tsaro da su kasance a ankare domin hana afkuwar lamarin.

Jaridar Vanguard ta ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022 suka kai hari ga Jirgin Abuja zuwa Kaduna a garin Katari ta Jihar Kaduna tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama.

Advertisement

Sai dai a wannan karon, Hukumar DSS ta fitar da sanarwar domin ta gargadi fasinjojin Jirgin da kuma mahukuntansa da su yi taka tsantsan a kan lamarin.

Haka ma hukumar ta ta bata shawarar cewa a karfafa na’urorin ɗauɗauka na zamani da kan sa ido kan hanyar dogon da wurin shingen sojoji ko Jami’an ƴan Sanda da kuma tura karin jami’ai domin daka ido akan Jirgin da ma hanyar.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *