Connect with us

News

Kamfanin Google zai horas matasa 20,000 fasahar yanar gizo a Najeriya.

Published

on

Kamfanin google

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Kamfanin Google ya sanar da shirin bai wa mata da matasa dubu 20 horo a kasar nan kan fasahar yanar gizo domin taimaka wa gwamnatin ƙasar cimma burin samar da ayyuka miliyan 1 da suka shafi fasahar zamani.

Advertisement

Kamfanin na Amurka ya kuma ce zai ba da tallafin dala miliyan ɗaya a kasar nan.

Rundunar ‘Yan sanda jahar katsina sun kashe ‘yan ta’adda, tare kwato tumaki 60

Wannan na zuwa ne bayan tattaunawar da daraktan kamfannin Google a Afirka ta yamma Olumide Balogun da mataimakin shugabna kasa Kasshim Shetti a Abuja.

Kashim Shettima ya ce gwamnatin shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu ta shirya tallafa wa matasa domin su baje kolin fasaharsu domin ci gaban wannan fannin a kasar.

Advertisement

A jawabin da shugaban kasar ya gabatar wa kasar makonni biyu da suka gabata ne, ya alƙawarta samar wa matasa miliyan ɗaya ayyukan yi musamman a ɓangaren fasohohin zamani.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *