Connect with us

News

Gwamnan Jahar Yobe Ya Amince da Miliyan N667m don Biyan ‘Yan Fansho

Published

on

Gwamanan Jahar yobe Mai Mala Buni

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da biyan ‘yan fansho na kananan hukumomi 17 dake jihar kamar yanda jaridar Daily Post ta rawaito.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mamman Mohammed, ya sanyawa hannu ranar Alhamis.

Hukumar Hisba ta gayyaci Gfresh Al’amin angon Sayyada Sadiya Haruna

A cewar sanarwar, gwamnan ya amince da kudi naira miliyan N667,045,441.22 domin biyan ‘yan fansho su 475 na kananan hukumomi hakkokin su.

Har ila yau, Buni ya bayar da amincewar ne bayan tantance masu karbar fansho a kananan hukumomi 17.

Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan na daga ci gaba da kokarin Gwamna Buni na ganin an daidaita kudaden fansho da ma’aikatan kananan hukumomin da suka yi ritaya suke bi.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement