Connect with us

News

Gwamnatin jahar Kano Ta Kaddamar Da Kwamitin Tantance Ma’aikata Kusan Dubu 10 da 800

Published

on

Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin mutum 22 domin tantance ma’aikata kusan dubu 10 da 800 da aka dauka aiki a karshen wa’adin gwamnatin da ta gabata ta Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Advertisement

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Baffa Bichi, ya ce kwamitin zai tabbatar da ko anbi ka’ida wajen daukar ma’aikata kusan dubu 10 da 800.

Gwamnatin Kano Ta Bayyana Damuwa Kan Yunkurin Bada Cin Hanci A Kotun Kararrakin Zabe

Kwamitin zai yi aiki bisa jagorancin shugaban hukumar daukar ma’aikata, Alhaji Umar Shehu Minjibir, kuma an baiwa kwamitin wa’adin makonni uku ya kammala aikinsa.

A martanin da ya mayar, Minjibir ya yi alkawarin cewa mambobin kwamitin za su yi iya kokarinsu don ganin sun kammala aikin a kan lokaci.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *