Connect with us

News

Kungiyar Dattawan Arewa Ta Bukaci Tinubu Ya Cire Takunkumin Da Aka Kakabawa Nijar

Published

on

Shugaban kungiyar Dattawan Arewa Ango Abdullahi

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Kungiyar Dattawan Arewa tayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya dage takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa Jamhuriyar Nijar.

Shugaban kungiyar Ango Abdullahi, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake amfani da karfi wajen maido da tsarin mulkin jamhuriyar Nijar, yana mai cewa da wuya a samu sakamako mai kyau.

Bai Kamata Ba Tunibu Ya Baiwa Dan Siyasa Ministan Tsaro Ba-Shehu Sani

Ya kuma jaddada cewa cire takunkumin zai taimaka wajen gudanar da shawarwari, don haka ya bukaci yin aiki da diflomasiyya.

Idan dai za a iya tunawa kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Tinubu ta sanya takunkumin hana wutar lantarki da kuma rufe kan iyakokin Nijar jim kadan bayan hambarar da zababben shugaban kasar Mohammed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement