Connect with us

News

Gobara ta kone kayayyaki na miliyoyin Naira a kasuwar Ibadan

Published

on

Gobara a kasuwar Ogunpa Labaowo da ke Agbokojo, Ibadan, babban birnin Jihar Oyo

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Wasu ’yan kasuwar Ogunpa Labaowo da ke Agbokojo, Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, a halin yanzu suna kidayar asarar da suka yi, sakamakon wata gobara da ta yi barna a sassan kasuwar a yau Juma’a.

Gobarar ta lalata kayayyakin da darajarsu ta kai na miliyoyin kudadi, wadda ta faro da sanyin safiyar Juma’a, kamar yadda jaridar DAILY POST ta rawaito

Indaranka:Matukin jirgin sama ya mutu a bandaki dauke da fasinjoji 271

Kayayyakin na miliyoyin naira, irinsu na’urorin hada-hada, katifu, da na’urorin gyaran mota na daga cikin kayayakin da gobarar ta kone.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Abdul-Jelil Oladimeji, wanda ya kware wajen gyaran motoci, ya koka da yadda ya yi asarar kayan aiki na miliyoyin.

Shugaban kungiyar injiniyoyin shuka ta Ogunpa Labaowo, Azeez Ibrahim, ya yi zargin cewa gobarar ta tashi ne a sakamakon karuwar wutar lantarki da aka samu a yankin.

Ibrahim, wanda ya ci gaba da bayyana cewa gobara ta lalata masu hada-hadar siminti da injinan su, ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement