Connect with us

News

Mutane 6,000 sun tsere daga muhallinsu sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Neja

Published

on

Ambaliyar ruwa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Mataimakin gwamnan Jihar Neja Yakubu Garba ya shaida cewa kimanin mutane 6000 ne suka tsere daga muhallinsu sakamakon iftala’in ambaliya ruwa da kuma ayyukan yan fashin daji a jahar .

Bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kaiwa shugaban Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA a birnin Tarayya Abuja.

Advertisement

Wani mutum dan shekara 50 ya kashe dan autansa a Jigawa

Wannan ziyara ta Mataimakin gwamnan na zuwa ne yayin yan fashin daji ke ci gaba cin karensu babu babbaka a wasu yankuna na jihar, a don haka ne ma ya miƙa buƙatar da a kai musu ɗoki.

Ya ƙara da cewa ambaliyar ruwa tana ci gaba da ɗaiɗaita Jihar don haka akwai buƙatar Hukumar ta shigo lamarin don samo bakin zarensa.

Ya ce “Jihar Neja tana fama da matsalolin tsaro daban daban wanda babu inda za mu kai kukanmu da ya wuce nan a halin da ake ciki”

Advertisement

“Ba’ada Zalika, hasashen yanayi ya nuna cewa akwai yiwuwar ta’azzarar ambaliyar ruwa a daminar bana wanda da ma mu mun daɗe fuskantar hakan a Jihar Neja”

Yakubu Garba bugu da ƙari ya ce a ɓangaren gwamnatin Jihar tana iya ƙoƙarinta domin tuni ake ci gaba da wayar da kan al’umma da su gagauta tashi daga inda iftala’in ya fi aukuwa don gudun aikin da-na-sani.

Da yake maida jawabi shugaban Hukumar NEMA ya ce hukumar kullum cikin ɗamara take na ganin ta baiwa dukkannin agaji ga waɗanda iftala’i ya shafa a fadin kasarnan.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *