Connect with us

News

Kungiyar Mawallafa Labarai A Intanet ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayi Abdullahi Yakubu na Jaridar Leadership

Published

on

marigayi Abdullahi Yakubu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Shugaban riko na kungiyar mawallafa jaridar yanar gizo ta Chartered Online, ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayi Abdullahi Yakubu, wakilin Jaridun Leadership na Jihar Kano, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Juma’a 18 ga watan Agusta, 2023.

Hakan na kunshe ta cikin wata Sanarwa mai dauke da sannun shugaban kungiyar na riko Abdullateef Abubakar Jos wanda kuma mawallafin jaridar SOLACEBASE ya raba wa manema labarai, ya ce rasuwar Abdullahi Yakubu babbar asara ce ga aikin jarida a Kano da ma Najeriya baki daya, duba da irin gudunmawar da ya bayar.

Advertisement

Tallafin Biliyan 180: Gwamnoni Ba Abin Yadda Bane Da Kuɗaɗe. NLC 

Kungiyar ta kuma jajantawa kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, da kuma kungiyar ‘yan jarida ta jihar Kano correspondent chapel.

Sanarwar ta kara da cewa ‘yan kungiyar Chartered Online Publishers ta Kano da shugabanninta sun samu labarin rasuwar babban abokin aikinsu cikin matukar kaduwa, tare da bayyana cewa Abdullahi Yakubu ya shahara da hakuri da jajircewarsa a aikin jarida tun zamanin da ya yi aiki a kamfanin buga jaridu na Triumph .

Kungiyar Chartered Online Publishers sun yi addu’ar Allah ubangaji ya baiwa iyalansa hakurin jure rashin.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *