Connect with us

News

Injiniyoyi Mata Sun Roki Tinubu Ya Sahale Su Gyara Matatun mai Cikin Shekara ‘Daya

Published

on

Injiniya mace a bakan aiki

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Kungiyar kwararrun Injiniyoyi mata ta Kasa APWEN tayi kira ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya baiwa injiniyoyi mata damar gyara matatun mai na kasa.

Shugabar kungiyar, Atinuke Owolabi ce ta yi wannan kiran yayin taron lacca da taron shekara-shekara na kungiyar a Legas.

Yadda ƙananan hukumomi 23 ke rayuwa cikin fitinar ‘yan bindiga

Owolabi ta ce injiniyoyi mata a Najeriya za su iya farfado da matatun mai gaba daya a cikin shekara 1 kacal.

Ta ce Najeriya na bukatar rage dogaro ga kwararrun kasashen waje tare da bada damammaki ga injiniyoyin cikin gida wadanda suke da kwarewa daidai ko suka wuce na kasashen wajen.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement