Connect with us

News

Ranar Yaki Da Cizon Sauro: Majalisa Ta Bukaci Gwamnati Ta Ayyana Dokar Ta-baci Kan Malaria

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.

Majalisar Wakilai ta tarayya ta bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci kan cutar maleriya, tare da misalta cutar a matsayin mai mummuke mutane sannu a hankali da ke janyo mutuwan ‘yan Nijeriya.

Shugaban kwamitin yaki da cutar zazzabin cikin sauro, tarin fuka, da cutar nan mai karya garkuwar jiki wato (HIV), na majalisar, Hon. Amobi Ogah, shi ne ya shaida hakan ta cikin sanarwar da ya fitar ga ‘yan jarida a Abuja ranar Lahadi domin raya bikin ranar yaki da cizon sauro ta duniya na 2023.

Atiku, Kwankwaso da Obi Su Na Tattaunawa Domin Kafa Gagarumar Jam’iyyar Adawa

Ana raya bikin yaki da cizon sauro ne a duk duniya a duk ranar 20 ga watan Agusta domin nazari da bibiyar hanyoyin dakile kisan da cizon sauro ke yi wa jama’a.

Manufar da ke cikin hakan shi ne domin wayar da kan jama’a da kuma daukan matakan kariya daga cutar tare da jawo hankalin hukumomi wajen daukan matakan da suka dace domin shawo kan cutar maleriya da ke addabar jama’a.

Ogah, dan majalisar mai wakiltar mazabar Isuiwuato/Umunneochi daga jihar Abia, ya ce, maleriya ta zama babban barazana ga kiwon lafiya, kuma akwai bukatar daukan dukkanin matakan dakile yawan mutuwa da ake yi a sanadiyyar cutar.

Ya ce, majalisar ta 10 za ta yi dukkanin mai yiyu wajen ganin an rage kaifin illar da cutar maleriya ke yi a Nijeriya.

“Kwamitinmu za ta yi aiki da hukumomin da suka dace wajen yaki da cutar maleriya kuma za mu tabbatar dukanin kudin da aka ware an yi amfani da su domin tabbatar da cimma manufar da ake so.

“A cewar hukumar lafiya ta duniya, kasashen Afrika hudu sune ke da rinjayen masu mutuwa sakamakon cutar maleriya. Nijeriya kuma ita ce ke kan gaba da kaso 31.3 cikin dari, yayin da jamhuriyyar Congo take biye mata da kaso 12.6 cikin dari sai kuma, Tanzania mai kaso 4.1, yayin da jamhuriyyar Nijar take da kaso 3.9 cikin dari.”

Ya ce, Nijeriya na bukatar kariya daga cutar malaria. Ya bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki da su tabbatar sun rage kaifin yaduwar cutar maleriya tare da kare jama’a daga illar da zazzabin cizon sauro ke janyowa.

Dan majalisar ya ce dukkanin kokarin da ya dace a yi wajen kawar da cutar maleriya ya kamata a yi hakan domin kula da kiwon lafiyan al’ummar Nijeriya.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement