Connect with us

News

Kano Poly ta ƙaddamar da Gudanar da shirye-shiryen BSc, PGD da kuma MSc,

Published

on

KANO STATE POLYTECHNIC

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

A kokarinta na samar da yanayi daban-daban na ilmantarwa da kuma kara damar samun ilimi ga matasan mu na hadin gwiwa, hukumar gudanarwar kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano (KSP) ta kulla hadin gwiwa da wata cibiya (Mona Institute of Hospitality, Tourism, Management and Research Development of Nigeria) don gudanar da bada takardar shaidar digiri ta BSc, digiri na biyu MSc, dama shaidar share fagen digiri na biyu wato PGD a turance.

Shirye-shiryen dai na ɗan lokaci a ƙarƙashin Daraktan Shirye-shiryen Part-Time na Jami’ar Fasaha ta Akintola, Ogbomoso.

Advertisement

Shetima zai yi balaguro zuwa kasar Afrika ta kudu

Da yake jawabi a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU), shugaban cibiyar, John Daniel ya bayyana jin dadinsa game da alkawura da himma da hukumar kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano ke nunawa wajen ganin an aiwatar da hadin gwiwar.

Ya jaddada cewa sun yanke shawarar yin hadin gwiwa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano ne bisa la’akari da ingancinta ta bangaren samar da dalibai masu kwarewa da ke ayyuka a sassan kasar nan daban-daban.

Shima da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban kwamitin, Dr. Muhammad Umar Kibiya wanda kuma shine shugaban kwamitin hadin gwiwa ya bayyana cewa, hadin gwiwar zai yi tasiri da kuma inganta cibiyar da ma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano dama kasa ba ki daya.

Advertisement

Da yake mayar da jawabi, shugaban makaranatar Dr. Kabir Bello Dungurawa ya yaba da kwazon matakin da cibiyar ta dauka na tantance Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano.

Ya nanata cewa hadin gwiwar zai baiwa dalibai da masu sha’awar bunkasa shaidarsu damar yin hakan a fannonin karatunsu daban-daban.

Ya kuma bukaci cibiyar da ta tabbatar da ka’idojin ilimi, tare da tabbatar da cewa hukumar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano ta himmatu wajen gudanar da wannan aiki.

Advertisement

A halin yanzu, duk shirye-shiryen da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano ya bayar za su kasance don PGD da MSc, yayin da aka amince da shirye-shiryen masu zuwa don BSc:

1) Bachelor of Science (BSc) Environmental Health:

a. Public Health

Advertisement

b. Community Health & Social Works with options in:

i- Community Development

ii- Social Welfare Care

Advertisement

iii- Occupational Health and Safety Management

iv- Industrial Social Welfare

v- Community Health

Advertisement

2) BSc in Transport Management with an option in:

i. Aviation Management

ii. Logistics Management

Advertisement

iii. Maritime Management

iv. Procurement Management

v. Supply Chain Management

Advertisement

vi. Port Operations Management

3) BSc Economics

4) BSc Insurance

Advertisement

5) BSc Entrepreneurship Studies

6) BSc Actuarial Science

7) BSc Mathematics

Advertisement

8) BSc Psychology and Behavioral Studies

9) BSc Sociology

10) BSc Environmental Management

Advertisement

11) BSc Political Science

12) BA English and Literacy Studies

13) BA History and International Studies

Advertisement

Ana sa ran shirye-shiryen za su fara a cikin zaman karatun 2023/2024.

Jaridar Internet ta Inda Ranka ta ruwaito bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban hulda da jama’a na kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano, Auwal Isma’il Bagwai, kuma aka aikewa da manema labarai.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *