Connect with us

News

Sai Da Ya Samu Izinin Shugabannin PDP Kafin Ya Karbi Matsayin Minista–Wike

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.

Sabon ministan birnin taraiyya Abuja, Nyesom Wike, Ya ce sai da ya samu izinin jagororin jam’iyyar PDP,kafin ya amince da tayin zama minista a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yayi masa.

Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar PDP sun rika kokarin ganin an dakatar da shi daga jam’iyyar,sakamakon alakar da yake da ita tsakaninsa da ‘yan jam’iyyar APC, da kuma amincewa da karbar matsayin ministan da ya yi.

Manyan ƙalubalan da ke gaban sabbin ministocin tsaron Najeriya

Sai dai a yayin taron manema Labarai da minista Wike ya yi a jiya, jim kadan bayan rantsuwar kama aiki, Ya tabbatar da cewar sai da ya rubuta wasika ga shugabannin jam’iyyarsa, cikinsu hadda mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iliya Damagum , Kuma ya samu amincewarsu na zama minista a gwamnatin Tinubu.

Sabon ministan Abujar ya yi barazanar rushe duk wasu gine-gine da aka yi wanda suka ci karo da taswirar birnin taraiyya Abuja.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement