Connect with us

News

Gwamnan Jahar Kano Zai Biya Wa Daliban BUK 7,000 Kudin Makaranta

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA.

 

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin biya wa daliban da ke karatu a Jami’ar Bayero (BUK) kimanin su 7,000 ’yan asalin Jihar kudin makaranta.

Advertisement

Babban mai taimaka wa Gwamnan a kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ne ya tabbatar da haka a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da maraicen Laraba.

Wata Mata Ta Kashe Dan Kishiyarta Dan Kimanin Kwanaki Hudu A Duniya A Bauchi

Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin biya wa ɗaliban jihar Kano da ke karatu a BUK su kimanin dubu bakwai kuɗin makaranta,” kamar yadda ya wallafa.

Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da daliban jami’ar ke ci gaba da kokawa da karin kudin da jami’ar ta yi.

Advertisement

A sakamakon karin, dalibai da dama sun rika neman gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa musu.

Hatta jami’ar ta Bayero sai da ta tsawaita wa’adin lokacin yin rajistar dalibai, kasancewar da dama daga cikinsu ba su iya kammalawa ba, saboda tsadar.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *