Connect with us

News

Gwamnatin Jahar Kano Zata Rabawa Mata Awaki Domin Dogaro Da Kai

Published

on

Akuya

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Gwamnatin jihar kano ta amince da biyan naira milyan 700 a matsayin kudin makaranta ga Dalibai yan asalin jihar Kano dubu bakwai dake karatu a jami’ar Bayero ta nan Kano.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Ya ce matakin wani bangare ne na saukakawa al’umma kan halin tsadar rayuwa da ake ciki.
Ya kara da cewar za’a tsara yadda matakan tsarin bada tallafin karatun zai kasance a nan gaba kadan.

YIN TALLACE TALLACE HARAMUN NE A BIRNIN ABUJA. Cewar ministan babban birnin wike

A wani bangaren kuma, Gwamnatin jihar kano na wani shiri na samar da shanu da Tumaki da kuma Awaki domin baiwa mata musamman a yankunan karkara,da zummar ganin sun dogara da kansu da kuma samun cigaban tattalin arziki.
Wannan dai wani bangare ne na rage radadin janye tallafin man fetir da aka yi, kamar yadda gwamnan jihar Kano,Abba Kabir Yusuf ya baiyana, a yayin zaman majalisar zartawa na wannan makon da aka yi jiya a gidan gwamnatin kano.
Ya kuma ce gwamnatin jihar Kano ta sayi hatsi na kimanin naira bilyan 1 da milyan 600 ,wanda ya hada da Gero da Masara da Shinkafa domin raba su kyauta ga al’ummar kano.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan kano,Sanusi Bature ya fitar, Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin taraiyya da ta sake yin nazari kan yadda ta yi tsarin rabon tallafin rage radadi a tsakanin jihohin kasar nan.
Sai dai ya godewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu kan tallafin da ta samar, tare da bada shawarar a baiwa jihar kano kaso mai tsoka kasancewar yawan jama’ar da take das u.

 

Arewa radio 

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement