Connect with us

Sport

Pepe zai iya koma wa Saudiyya,Man City za ta sayo Nunes

Published

on

Matheus Nunes

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Manchester City na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasan tsakiya na ƙasar Portugal Matheus Nunes, mai shekara 24 daga Wolves. (Athletic)

Ba lallai ne Wolves su bar Nunes ya bar kulob ɗin ba, daidai lokacin da aka kusa rufe kasuwar cinikin ‘yan ƙwallo, sia dai fa idan Manchester City za ta zuba mahaukatan kuɗi don sayen ɗan wasan. (Express & Star)

Gwamnan Jahar Kano Zai Biya Wa Daliban BUK 7,000 Kudin Makaranta

City ɗin ta koma zawarcin ɗan wasan tsakiyar Crystal Palace daga Ingila, Eberechi Eze, mai shekara 25, bayan ta janye daga zawarcin ɗan wasan tsakiya na Brazil, mai taka leda a West Ham, wato Lucas Paqueta mai shekara 25. (Times)

Fluminense ba za ta sayar da ɗan wasan tsakiyanta na ƙasar Brazil Andre, a bana ba, duk da sha’awar sayen matashin mai shekara 23 da ƙungiyoyin Liverpool da Fulham da kuma Sporting Lisbon ke yi. (O Globo – in Portuguese)

Kungiyar Arsenal da ɗan wasan gabanta na ƙasar Ivory Coast, Nicolas Pepe, mai shekara 28, sun fara tattaunawa a kan yunƙurin tafiyarsa zuwa Saudiyya, bayan ya yi watsi da damar koma wa Besiktas. (RMC via Metro)

Chelsea za ta buƙaci ɗan wasan gabanta na ƙasar Belgium, Romelu Lukaku, mai shekara 30, ya amince da wani tayin koma wa Saudiyya, idan ya kasa cimma matsaya da wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Turai. (Talksport)

Juventus na son ta biya Chelsea fam miliyan 35 a kan Lukaku, amma kulob ɗin na Italiya ya dogara ne a kan kuɗin da za su samu fam miliyan 50 daga cinikin ɗan wasan gaba na ƙasar Sabiya, Dusan Vlahovic mai shekara 23, kafin su iya kawo kuɗin. (Standard)

Kulob ɗin West Ham ya kuma fara tattaunawa da Sevilla a kan ɗan wasan tsakiya na Morocco, Youssef En-Nesyri, mai shekara 26. (Sky Sports)

Brentford ta yi ƙari a kan tayin da ta yi wa ɗan wasan gefen Fiorentina, Nico Gonzalez, sai dai daga kulob ɗin na Serie A, har ɗan wasan mai shekara 21 na ƙasar Sifaniya babu mai sha’awar daidaitawa a kan cinikin. (Football Italia)

Sheffield United ta kusa kammala cinikin fam miliyan 18.5 don ɗauko ɗan wasan gaba mai kai hari na Aston Villa, Cameron Archer mai shekara 21. (Guardian)

Tottenham sun yi watsi da yunƙurin Barcelona na ɗaukar ɗan wasan tsakiya mai kai hari daga Argentina, Giovani Lo Celso, mai shekara 27, a matsayin aro. (Sport – in Spanish)

Hamshaƙin ejan nan Jorge Mendes zai isa Barcelona, ga alama don kammala cinikin ɗaukar ɗan wasan baya na ƙasar Portugal mai shekara 29, Joao Cancelo daga kulob ɗin Manchester City zuwa Nou Camp. (AS – in Spanish)

Burnley da Granada dukkansu suna rawar jiki don cimma yarjejeniyar ɗauko ɗan wasan baya na Manchester United ɗan ƙasar Sifaniya, Alvaro Fernandez mai shekara 20. (Mirror)

Everton ta shiga kiki-kaka a tattaunawar da suke yi da Southampton game da cinikin ɗan wasan gaba na Scotland, Che Adams, mai shekara 27, amma dai ba za su ci gaba da yunƙurin sayen ɗan wasan gaba na kulob ɗin Troyes ɗan asalin Guinea-Bissau, Mama Balde mai shekara 27 ba. (Liverpool Echo)

 

BBC

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement