Connect with us

News

Wata Mata Ta Kashe Dan Kishiyarta Dan Kimanin Kwanaki Hudu A Duniya A Bauchi

Published

on

Sandar kotu

DAGA AISHA MUHAMMAD 

Wata mata mai suna Furera Abubakar mai shekaru 24 a duniya ta kashe dan kishiyarta dan kimanin kwanaki hudu a duniya a kauyen Bantu dake cikin karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.
Kakakin rundunar ‘Yan sanda a jihar SP Ahmed Wakil shi ne ya tabbatar da kama wacce ake zargin cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata.

Wakil, yayi bayanin cewa an kai rahoton faruwar lamarin zuwa ofishin yan sanda dake Ningi a ranar 19 ga watan Augusta 2023, kwanaki bayan haihuwar jaririn.

Advertisement

Mutum 17 Ne Suka Mutu Akan Gadar Jirgin Kasa Da Ta Karye

SP Wakili, ya kara da cewa yanzu haka ana cigaba da gudanar da bincike inda daga bisani za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *