Connect with us

News

Adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Mashako a Kano ya kai 100.

Published

on

Cutar mashako

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Mashako a jihar Kano ya kai 100.

Alkaluman bayanan da Cibiyar dakile yaduwar Cututtuka ta kasa, NCDC ta fitar a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata, ya sha banban da adadin mutanen da suka mutu saboda cutar su guda 76 da aka samu a watan Yunin bana.

Advertisement

Dillalan Man Sunce Za’a Iya Samun Tashin Farashin Man Fetir

Sabbin bayanan na zuwa ne a yayin da gwamnatin jihar kano ta ce tana bukatar alluran rigakafin da bai gaza miliyan shida ba domin yaki da bazuwar cutar ta Mashako.

Jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan wadanda suka kamu da cutar Mashako a kasar nan, inda mutane dubu 1 da 207 aka tabbatar da sun kamu da cutar daga cikin mutane dubu 3 da 234 da aka yiwa gwajin cutar ta Mashako.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *