Connect with us

News

Rundunar Yan sanda sun kama wani makiyayi da ake zargi da yanke hannun manomi a Bauchi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI           

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun kama wani matashi dan shekara 15 mai suna Adamu Ibrahim da ke kauyen Jital da ke kan hanyar Gombe bisa zarginsa da yanke hannun wani manomi sakamakon rashin jituwa da suka samu.

Jaridar Daily post ta rawaito cewa wanda ake zargin ya sha shiga gonakin wanda yanke hannun a  lokacin da yake kiwon shanunsa.

Advertisement

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Mohammed Wakil, ya fitar a ranar Asabar ta bayyana cewa, jerin korafe-korafen da aka yi wa mahaifin wanda ake zargin na kutsawa cikin gonakin  miutane na shinkafa.

“Bincike ya nuna cewa a ranar 24 ga watan Agusta, 2023, wanda ake zargin yana dauke da sanda da adduna, yayi mummunar barna tare da lalata amfanin gonakin da har yanzu ba a tantance ba.

“An samu rashin jituwa, inda wanda ake zargin ya daba wa wanda aka yankawa hannu  wuka bayan ya nemi ya bar gonarsa.

Advertisement

“Da samun wannan rahoton, kwamandan yankin, babban birnin tarayya, ya dauki matakin gaggawa tare da kara daukar matakan kariya don dakile al’amuran da ka iya haifar da rikicin makiyaya da manoma a yankin, ya kuma ba da umarnin kama wanda ake zargin,” in ji Wakil.

Ya kara da cewa, an garzaya da wanda abin ya shafa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin kula da lafiyarsa, kuma yana karbar magani.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *