Connect with us

News

Dole Ne Daukar Mataki Mai Tsauri Domin Dora Najeriya Kan Turbar Cigaba – Tinubu

Published

on

DAGA NUSAI ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Shugaba Bola Ahamd  Tinubu ya ce Najeriya ba za ta dore  cikin yanayin tattalin arziki mai rauni ba, wanda ya sa kasarnan ke yin amfani da kashi 90 na kudaden shigarta wajen biyan basussukan waje a cikin kalubalen cigaba.

Advertisement

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Abuja yayin da yake bude taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin ta kasa a babban filin wasa na Cif MKO Abiola.

Doka Bata Hanani Rike Mukamin Minista Ba Saboda Aikin Yiwa Kasa Hidima -Hannatu Musawa

Shugaban ya bayyana cewa dole ne a yanke hukunci mai tsauri domin dora  kasarnan a kan hanyar ci gaba, duk da radadin farko da gyare-gyare masu ma’ana ke kawowa.

Tinubu ya bayyana cewa wadatar da ‘yan Najeriya ke bukata zata faru ne kawai da zarar an kawar da talauci daga cikin al’umma tare da hadin gwiwar shugabannin kamfanoni masu zaman kansu na Najeriya.

Advertisement

Ya sake sabunta kudirinsa na tunkarar matsalar albashin jami’an shari’a da masu aiki a bangaren shari’a, inda ya ce dole ne a fara gyaran shari’a na gaskiya da albashi mai kyau da  duniya ke tafiya akai da alawus-alawus.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *