Connect with us

News

Gwamna Inuwa ya bada umarnin rufe gidajen rawa a Jahar Gombe

Published

on

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayar da umarnin rufe duk wani gidan rawa da ake kira ‘Gala Houses’ a cikin jihar nan take.

Gwamnan ya kuma bada  umarcin cewa  dukkan hukumomin tsaro da su tabbatar da bin umarnin.

Advertisement

SEMA: Akalla gidaje 700 da gonaki 700 ne ambaliyar ruwa ta lalata a Bauchi

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya fitar ranar Litinin.

A cewar Njodi, matakin ya biyo bayan wasu korafe-korafe da jama’a suka yi a kan ayyukan lalata da laifuka da kuma tabarbarewar tsaro da ake tafkawa a irin wadannan gidajen rawa na dare.

Ya ce, bisa wannan umarnin, rundunar ‘yan sandan, da  kuma Civil Defence da kuma Operation Hattara, suna sa ran za su gaggauta tattara jami’ansu domin aiwatar da wannan umarni tare da tabbatar da bin doka da oda.

Advertisement

Daga cikin gidajen Gala da abin ya shafa sun hada da: Jami’a Gidan Wanka, dake Mile 3 Road Yola, Gombe, gidan wasan kwaikwayo na White House (Babban Gida) dake New Mile 3 Road Yola, Gombe; Gidan Lokaci General Merchant, dake Mile 3 Reservoir Road, Gombe da Farin Gida Entertainment II dake Wuro Karal, Kalshingi Road, Gombe, da dai sauransu.

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *