Connect with us

News

Har Yanzu Tinubu Nada Tambayoyin Amsawa Akan Karatunsa – Atiku

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nanata cewa shugaba Bola Tinubu yana da tambayoyi da zai amsa game da tarihin karatunsa.

Da yake magana ta cikin wani rubutu a dandalin sada zumun na Twitter, Atiku ya ce shugaban kasar a shekarar 1999, ya yi ikirarin cewa ya yi makarantar firamare a Legas da makarantar sakandare a Ibadan kafin ya wuce Jami’ar Jihar Chicago ta Amurka.

Advertisement

Iyayen Marayu A Jihar Kano Na Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa

Amma a shekarar 2023, shugaban ya mika takardar shaidar kammala karatunsa na jami’a ne kawai ba tare da ambaton makarantun firamare da sakandare ba.

Atiku ya kara da cewa ya shiga rudani kuma yana son sanin yadda shugaban kasa Tinubu ya gudanar da karatun jami’a ba tare da makarantun firamare da sakandire ba.

Takardun makaranta na shugaba Tinubu na ɗaya daga cikin batutuwan da ake takaddama a Amurka da kuma a Kotun kararrakin zaɓen shugaban Ƙasa.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *