Connect with us

News

Kasar Kamaru Ta Gargadi Gwamnatin Najeriya Akan yiyuwar Samun Ambaliyar Ruwa A Wasu Jahohin Kasar nan

Published

on

Ambaliyar ruwa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Akwai yiyuwar wasu jihohi a Najeriya za su fuskanci ambaliyar ruwa nan da kwanaki masu zuwa yayin da Kamaru ke shirin bude madatsar ruwa ta Lagdo da ke gabar kogin Benue.

Jihohin a cewar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, sun hada da Adamawa, Taraba, Benue, Nasarawa, Kogi, Plateau, Gombe da Bauchi.

Dakta Labaran ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa cika alkawuran da ya dauka na kiwon lafiya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, a cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Agusta, ta sanar da hukumar NEMA, sanarwar bude madatsar ruwan da aka yi a kasar ta Kamaru.

Wasikar tace idan lokacin sakin ruwan ya yi, hukumomin dake kula da madatsar Lagdo za su sake ruwan daki daki domin dakile duk wata barnar da ke iya biyo baya ga mazauna yankunan dake bakin kogin a cikin Kamaru da kuma Najeriya.

Gwamnatin Kamaru ta bayyana fatan ganin hukumomin Najeriya sun yi amfani da wannan sanarwar domin fadakar da jama’a da kuma daukar duk matakan da suka dace dan kaucewa barnar dake iya biyo baya.

A duk shekara mazauna gabar kogin Benue a Najeriya kan tafka asarar rayuka da kuma dukiyoyi sakamakon sakin ruwan daga madatsar Lagdo idan ba’a fadakar da su ba.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement