Connect with us

News

GWAMNATIN KANO TA TSARA HANYOYIN WARWARE MATSALOLIN BASHIN DA MASU SAYAR DA MAGUNGUNA KE BIN DMCSA

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA.

 

Domin magance wasu daga cikin matsalolin da suka dabaibaye Hukumar Samar da Magunguna (DMCSA), gwamnatin Kano ta karkashin Ma’aikatar Lafiya ta Jiha ta shirya zama na musamman da wasu wakilan masu samar da magunguna.

Taron, wanda aka gudanar a harabar hukumar, yana da manufar tsara hanyoyin da za a warware dimbin bashin da wasu samar da magunguna ke bin hukumar, da kuma lalubo hanyar da za a bi don tabbatar da samar da ingantantun magunguna domin bunkasa lafiyar mutane jihar Kano baki daya.

Tsadar rayuwa ta sanya wasu iyaye a kano sun ragewa ya’yansu ranakun zuwa makaranata.

Da yake jawabi, mai girma Kwamishinan Lafiy na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana wa masu samar da magungunan cewa gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta karbi hukumar ne a wani mawuyacin hali na rashin kudi, yana mai tabbatar da cewa ma’aikatar lafiya ta jiha ta dauki tsattsauran matakan kawo karshen wadannan matsaloli da hukumar ke fuskanta.

Kwamishin yakara da cewa daga cikin matsalolin da hukumar ke fama da su akwai tarin bashi da masu samar da magunguna ke bin DCSMA da hukumar samar da da ya kai kusan Naira biliyan daya da miliyan dari biyu (N1.2b).

Shi ma a nasa bayanin, Babban Darakta na Hukumar Samar da Magunguna ta jihar Kano, Pharm. Gali Sule ya bayyana makasudin samar da hukumar da suka hada da samar da magunguna masu inganci, isassu kuma cikin farashi mai sauki ga dukkan asibitoci mallakin gwamnatin jihar Kano.

Shi ma da yake magana a maimaikon masu samar da magunguna da suka halarci taron, Ben Ochigbo ya yaba wa gwamnatin jiha da ma’aikatar lafiya karshin jagorancin kwamishina bisa goyon bayan da suke bayarwa don ciyar da DMCSA gaba.

Sannan sun jaddada kudirinsu na ci gaba da huldar kasuwanci da DMCSA domin sanar da ingantattun magunguna marasa yankewa kuma cikin farashi mai rahusa.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement