Connect with us

News

Shiru Ba Tsoro Ba Idan Lokaci Yazo Wike Zai Fuskanci Kora Ba Dakatarwa Ba Daga PDP – Daniel Bwala

Published

on

Daniel Bwala

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Tsohon mai magana da yawun Majalissar yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2023, Daniel Bwala, yace za’a kori ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike daga jam’iyyar PDP a lokacin da ya dace.

Advertisement

Bwala ya baiyana hakan ne a gidan Talabijin na Channels a daren jiya, kwana guda bayan Wike, tsohon gwamnan jihar Rivers, ya sha alwashin cewa babu wanda zai iya korarsa daga jam’iyyar PDP.

Ku Magance Cutar Dake Haifar Da Juyin Mulki Ba Alamomin Cutar Ba – Atiku Ya Aika Sako Ga Shugabannin Afirka

Bwala ya ce shiru da jam’iyyar ke yi ba rauni ba ne, ya kara da cewa jam’iyyar ta san abin da take yi kuma a lokacin da ya dace ba wai kawai za a dakatar da Wike ba matakin zai kasance na kora daga PDP baki daya.

Advertisement
Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *