Connect with us

News

Buhari maɓarnaci ne, ya kashe kashi 90 na kudaden shigar Najeriya akan biyan kuɗin ruwa – Obasanjo

Published

on

Buhari Obasanjo

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

Advertisement

 

 

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya zargi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ɓarnatar da kuɗin ƙasa a shekaru takwas da ya yi ya na mulki.

Advertisement

Obasanjo ya yi wannan zargin ne yayin wata hira da jaridar TheCable ta buga a jiya Litinin.

Obasanjo ya ce duk da ya san da cewa Buhari ba shi da ilimin tattalin arziki, bai taba tunanin zai zama maɓarnacin kudi haka ba.

“Kwanakin baya Tinubu ya ce ba zai amince da kashe kashi 90% na kudaden shiga don biyan kuɗin ruwa na basussukan da ake bin Nijeriya ba. Ban kashe kashi 90% ba lokacin da na shiga duniya don neman a yafe min wasu basussuka.

Advertisement

Kuna tunanin wani zai ba ku bashin yau? amma Buhari ya ke ta ɓarnatar da kuɗi haka. Na san Buhari bai fahimci tattalin arziki ba.

“Na sanya hakan a cikin littafina. Amma cewa shi ma yana iya yin sakaci, ban sani ba. Wa za ka je yau ka nemi alfarma yai maka?” in ji Obasanjo

Share
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *