Connect with us

News

Tinubu Ya Tafi Kasar Indiya Yayin Da Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Zabensa A Gobe

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, Bai damu da yadda zata kaya a hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa zata yanke a gobe ba.

A hirarsa da gidan Talabijin na Channels a daren jiya, kakakin shugaban kasa Ajuri Ngelale ,Ya ce shugaban kasar baya kallon wata barazana dangane da hukuncin kotun.

Kungiyoyin Kwadago Ta Kasa NLC Sun Fara Yajin Aikin Gargadi.

Haka zalika ya ce shugaban kasar nada kwarin gwiwa akan hukuncin da kotun zata yanke, la’akari da kwararran hujjojin da bangarensa ya gabatar.
Bugu da kari ya ce shugaban kasar nada kwarin gwiwa ga bangaren shari’a, wanda ya ce yana da yakinin za’a sake tabbatar masa da nasararsa da ya samu.

Kungiyoyin Kwadago Ta Kasa NLC Sun Fara Yajin Aikin Gargadi.

Gwamnan jihar Borno da ke arewacin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da shirin shuka bishiya miliyan ɗaya da dubu 200 a faɗin jihar.

An ƙaddamar da shiin na 2023 a asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Borno a yau Litinin da zimmar rage kwararowar hamada da kuma sauran matsalolin muhalli, a cewar gwamnatin jihar.

“Taken shirin na bana shi ne ‘Trees for Resettlement’, wanda ya yi daidai da babban taken Majalisar Ɗinkin Duniya na ‘Let’s Green Our City’,” in ji wata sanarwa.

Gwamnan ya nemi mazauna jihar su dinga amfani da iskar gas wajen girki maimakon ƙona itatuwa.

“Idan ba a ɗauki mataki kan sare itatuwa ba, wata rana za mu wayi gari duk faɗin jihar Borno ya zama hamada. Muna sane cewa ‘yan bindiga sun sa mun rasa kashi 80 cikin 100 na bishiyoyinmu,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa an sare dukkan bishiyoyin da ke dazukan ne saboda matsalolin tsaro, “wasu kuma saboda itacen girki”.

Share
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement
Advertisement